Kawancen da kasar Saudiyya take jagoranta ya kaddamar a ranar Lahadi da wani bincike kan zarge zarge cin zarafi a kasar Yemen, har ma game da mutuwar fararen hula da ba su ji ba su gani bisa kuskuren abokan yaki, in ji kamfanin dillancin labarai na Al Arabiya.
Hedkawatar kawancen ta bayyana wadannan zarge zarge da kafofin watsa labaru da kungiyoyin agaji suka ambato dake shafar mutuwar fararen hula da ba su ji ba su gani ba dalilin harbi daga bangaren abokan yaki, a matsayin wani abin nuna damuwa da kuma rashin bin ka'adoji.
Kawancen ya jaddada girmama duk kudurori da dokokin kasa da kasa, tare da sanar cewa, zai kaddamar da wani bincike kan wadannan zarge zargen cin zarafi na 'yancin dan Adam, tare da bayyana cewar, za a fitar rahoton bincike na karshe, kana kuma zai kunshe da duk fannonin da abin ya shafa.
Hedkwatar kawancen ta kuma ba da amincewarta ga kwamitin bincike domin ya zabi kwararru da za su taimake shi wajen gudanar da bincike.
Tawagar za ta isa wurare daban daban domin tattare bayanai. Wani asibitin agajin jin kai na MSF da ya fuskanci luguden wuta daga abokan yaki a Yemen.
Kawancen ya jaddada cewa, asibitin na cikin yankin tsaro, a lokacin da yake neman abokan gaba a kusa da asibitin, lamarin da ya janyo barna daga wajen asibitin. Daga karshe dai kawancen ya samu tattaunawa tare da ma'aikatan MSF kan matakan da za a dauka domin kaucewa irin wadannan hadura a gaba. (Maman Ada)