in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani harin makami mai linzami ya hallaka dakarun Saudia 10 a Yemen
2015-09-06 10:29:45 cri

Rahotanni daga lardin Maarib daka kasar Yamen, na cewa, a kalla dakarun kasar Saudia 10 ne suka hallaka, sakamakon wani hari da mayakan Houthi suka kai kan sansanin sajojin Saudian dake lardin.

Wani gidan talabijin dake yankin ya bayyana cewa, baya ga sojojin Saudia, harin da mayakan na Houthi suka kaddamar da makami mai linzami a ranar Juma'a, ya kuma hallaka dakarun hadaddiyar daular Larabawa su 45, da kuma wasu sojojin kasar Bahrain su 5.

An ce, makamin mai linzami ya fada ne kan wani wurin ajiyar makamai, wanda ke sansanin dakarun hadin gwiwar, lamarin da ya haddasa babbar fashewa da ta hallaka sojojin hadakar.

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin dakarun hadin gwiwar Birgediya Ahmed Asiri, ya ce, sojoji 10 ne suka rasa rayukansu, yayin da aka sallami da dama daga wadanda suka jikkata daga asibiti bayan da suka samu sauki. Wannan ne dai hari mafi muni da dakarun Houthi suka kaiwa rukunin sojin da Saudia ke jagoranta tun fara aikin tawagar a watan Maris.

Duk da hakan, kakakin rundunar ya ce, harin ba zai hana su ci gaba da taimakawa kasar Yemen a yunkurinta na sake farfadowa, da wanzar da zaman lafiya ba.

Dakarun hadin gwiwar Saudiar sun mai da martani da hare-hare ta sama kan dakarun na Houthi, a sassa daban daban na kasar ta Yemen.

Tun Cikin watan Maris ne dakarun na hadaka suka fara kaddamar da hare-hare kan mayakan 'yan tawayen kungiyar Houthi, a wani mataki na goyon bayan hanbararriyar gwamnatin kasar. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China