in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD: Mummunan fari ya raba mutanen Somalia 714,000 da muhallansu
2017-06-02 10:28:42 cri

Wani rahoto na baya bayan nan da ofishin kula da jin kai na MDD OCHA ya fitar ya nuna cewa, kimanin mutanen kasar Somalia dubu 714 ne matsalar mummunan fari ya daidaita daga muhallansu zuwa sassa daban daban tun daga watan Nuwamba na shekarar 2016.

Rahoton ya ce, kashi 65 cikin 100 na mutanen da suka bar muhallan nasu 'yan kasa da shekara 18 ne.

OCHA ya ce, matsalar farin ta ninka har sau uku, ga matsalar tsaro da barkewar cutuka, sun kasance wasu daga cikin matsalolin da suka jefa mutanen cikin matsanancin hali, musamman mata da kananan yara, da kuma wasu iyalan da mata ne ke jagorantarsu, wadanda suke fama da matsalolin barazanar cin zarafi, da tilastawa da yin garkuwa.

Ofishin kula da jin kai ta MDD ya ce, watan Mayu ya kasance wani muhimmin lokaci da ake samun karuwar sabbin mutanen da ke rabuwa da muhallansu a yankunan kasar ta Somalia.

Wani kwamitin sa ido wajen kare 'yan gudun hijira na MDD (PRMN) ya danganta karuwar mutanen da yanayin ruwan sama a Somalia, kana a bangare guda kuma akwai matsalar da ruwan saman ke haifarwa wajen rashin samun hanyoyin wucewa da mutanen ke fuskanta a lokacin damina.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China