in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani jirgin ruwa ya sake hallaka mutane 7 a tekun Libya
2015-08-31 11:16:12 cri

A ranar Lahadin nan hukumar ba da agajin gaggawa ta Red Crescent ta kasar Libya ta tabbatar da cewar, kimanin bakin haure 7 ne suka mutu a tekun al-Khoms na Libya.

Rahotanni sun ce, mai magana da yawun hukumar ba da agaji ta Libyan Muhammad Al-Misrati ya tabbatar da cewar, an samu gawawwakin bakin haure 7 da suka kife a jirgin ruwan, to sai dai bai yi karin haske ba kan adadin mutanen da jirgin ruwan ke dauke da su.

Hadarin na ranar Lahadi ya faru ne bayan afkuwar makamancinsa a ranar Alhamis ta makon jiya, inda jirgin ruwa ya kife da bakin haure 400 a tekun Zuwarah dake yammacin kasar Libya a kan hanyarsu ta zuwa Turai, kuma a kalla mutane 200 ne aka zaton da mutuwarsu.

Wata sanarwa daga jami'an lura da jiragen ruwan kasar ta ce, sama da gawawwaki 100 aka tsamo da suka hada da mata da kananan yara, sannan an samu nasarar ceto mutane 198 da ransu.

Kasar Libya ta fada cikin tashin hankali da tabarbarewar tsaro ne tun bayan kifar da gwamnatin Muammar Gaddifi a shekarar 2011, kasar wacce ke arewacin Afrika ta zama tamkar wani sansani ne wanda bakin haure ke kwarara ta gabar tekun Meditareniya zuwa kasashen Turai.

Hukumar lura da bakin haure ta duniya ta ce, a kalla mutane dubu 150 ne suka tsallaka zuwa Turai daga teku a tsakiyar watan Yulin shekarar 2015, kuma galibinsu sun fito daga Libya.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China