Babban daraktan shirin tsugunar da jama'a na MDD Joan Clos, ya ce nahiyar Afrika na cikin wani muhimmin lokaci, kuma nasarar da kasar Sin ta samu wajen raya birane da samun ci gaba, abun koyi ne ga nahiyar.
Joan Clos ya ce, da matsakaicin alkaluman GDP na Afrika dake kimanin dala 2,000 da yadda halin da tattalin arzikin nahiyar ke ciki, ya so ya yi kama da yadda kasar Sin ta kasance a lokacin da ta kaddamar da shirin bude kofa ga kasashen waje a shekarar 1978.
Ya kara da cewa, matakan da gwamnatin kasar Sin ta dauka wajen samar da ci gaba cikin shekaru 5 da suka gabata, sun yi matukar burge shi.
Ya kuma yabawa goyon bayan da kasar Sin ta ba taron MDD kan sauyin yanayi a Paris a shekarar 2015, da kuma nasarar da ta samu wajen magance matsalar a ciki da wajen kasar.
Ya ce, matakai da dabarun da Sin ta dauka kari ne kan nasarar da ta samu wajen samar da masana'antu a birane.
Har ila yau, ya ce yana da kyakyyawan fata kan makomar kasar Sin da kasashen Afrika, yana mai cewa dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu ta samu ci gaba cikin shekaru 5 da suka gabata. (Fa'iza Mustapha)