Jakadan kasar Sin a Zambia Yang Youming, ya ce karuwar adadin dalibai dake neman yin karatu a kasar Sin, alama ce da ke bayyana ingantaccen ilimi da kasar ke bayarwa.
Yang Youming, ya ce kasar Sin ta ji dadin yadda kasashen Afrika ke yabawa da tsarin iliminta, yana mai alkawarin kasar za ta ci gaba da samar ingantaccen ilimi.
Yayin wani taron manema labarai a jiya, jakadan ya gabatar da wasikar godiyar da dalibai 11 cikin 26 da suka yi karatu a kasar Sin cikin shekarar da ta gabata suka bayar. Daliban dai sun yi karatu ne a fannin wake-wake da raye-raye karkashin wani shirin da uwargidan shugaban kasar Sin Peng Liyuan da takwararta ta Zambia Esther Lungu suka shirya.
Yang Youming, ya kuma gabatar da wata wasika da uwargidan shugaban kasar Sin ta bayar a matsayin martani ga wasikar daliban.
Jakadan na kasar Sin ya ce, kasarsa ta zama muhimmin wuri ba kadai ga matasan Zambia dake son karatu a ketare ba, har ma da Afrika baki dayanta, yana mai cewa, kasar Sin ita ce ta biyu bayan Faransa dake jan hankalin dalibai daga nahiyar Afrika.
Ya ce, musaya tsakanin jana na da muhimmanci domin tana ba da damar koyon al'adun wasu kasashe, yana mai cewa, kasar Sin na sa ran ganin karin dalibai daga Afrika na zuwa neman ilimi a jami'o'inta. (Fa'iza Mustapha)