in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da kasashen Afirka na fatan cin gajiya tare a fannin hadin gwiwar tattalin arziki
2017-11-29 09:38:54 cri

Wakilai mahalarta taron tattaunawa, game da bunkasa hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da takwarorin ta na nahiyar Afirka, sun bayyana kyakkyawan fatan bunkasa alakar sassan biyu.

Hakan dai na kunshe ne cikin jawaban mahalarta dandalin CAIF da aka kammala a jiya Talata a birnin Marrakech na kasar Morocco. Taron dai na CAIF na wannan karo shi ne irin sa na biyu da aka gudanar, ya kuma samu halartar manyan jagororin hada hadar cinikayya da kasuwanci kusan 500 daga Sin da kasashen Afirka, wadanda kuma suka yi musayar ra'ayoyi a fannin cinikayya da zuba jari.

Rahotanni sun nuna cewa, makalolin da aka gabatar yayin taron na wannan lokaci, sun nazarci tasirin shigar da kudade cikin harkokin raya tattalin arzikin kasashen nahiyar Afirka, karkashin shawarar nan ta ziri daya da hanya daya, da ma yadda hakan zai tallafawa nahiyar a fagen raya masana'antu.

A wani bangare na taron, an gudanar da mahawarori na karin haske, game da tsare tsare da yanayin gudanar da tattalin arzikin kasar Sin da na kasashen Afirka, tare da muhallin da sassan biyu ke samarwa domin aiwatar da hadin gwiwa.

Da yake tsokaci game da taron na wannan karo, ministan ma'aikatar masana'antu, da cinikayya, da zuba jari da raya tattalin arziki na kasar Morocco Hafid Elalamy, ya ce hakan wani babban mataki ne da kasar sa ta dauka, domin ba da gudummawa ga hadin gwiwar sassan biyu. Mr. Elalamy ya ce, fatansa shi ne kasashe masu tasowa, su samu zarafi na tattaunawa, tare da bunkasa alakar kasar Morocco da Sin da sauran kasashen Afirka.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China