in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya: Ana samun nasara game da yaki da cin hanci
2017-11-28 09:20:58 cri

Ministan watsa labarai a tarayyar Najeriya Lai Muhammad, ya ce gwamnatin kasar mai ci na iya kokarin ta, na ganin ta magance mummunar dabi'ar nan ta cin hanci da rashawa tsakanin al'ummar kasar.

Lai Muhammad wanda ya bayyana hakan ga manema labarai a birnin Abuja, fadar mulkin kasar, ya ce duk da cewa ana fuskantar tarin kalubale game da wannan aiki, amma hakan ba zai dakile kwazon gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari na ganin ta kawo karshen wannan ta'ada ba.

Ya ce, a karkashin manufar, yanzu haka Najeriya ta kara yawan kudaden ajiyar ta na ketare da kusan dalar Amurka miliyan 500. Kana asusun tsumin kasar ma ya karu daga dalar Amurka biliyan 23 zuwa dala biliyan 35. A daya hannun kuma, an dakatar da biyan kudaden tallafin man fetur da yawan su ke kaiwa biliyoyin daloli.

Alkaluman kididdiga sun nuna cewa, mahukuntan kasar sun samu nasarar kwato kudade da yawan su ya kai dala biliyan 2.9 daga masu rub da ciki kan dukiyar kasar. Rahotanni na cewa, an karbe kudade da yawan su ya kai dalar Amurka miliyan 43, da gidaje 56, daga hannun wani tsohon gwamnan kasar.

Gwamnatin Najeriyar ta kuma bullo da wani shiri na ba da tukuici, ga duk wadanda ya tona asirin masu wawure dukiyar kasar, lamarin da share fagen gano dunbin kudaden da aka sace, wadanda yawan su ya kai dala miliyan 151 daga wasu sassa 3 kacal da aka bincika.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China