in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude cibiyar nazarin tekun Atilantika a Najeriya
2017-12-05 09:10:20 cri

Ministan kimiyya da fasaha na Najeriya Ogbonnaya Onu ya bayyana cewa, gwamnatin Najeriya za ta bude wata kafa ta hadin gwiwa tsakanin masana daga sassa daban-daban na duniya domin shiga a dama da su a harkokin nazari da kuma binciken tekun Atilantika, teku na biyu mafi girma a duniya.

Ministan wanda ya bayyana hakan yayin wani biki a Abuja, fadar mulkin Najeriya, wanda ya zo dai-dai da bikin bude cibiyar nazarin tekun Atilantika, ya ce, Najeriya za ta gayyato kwararru, kana tana maraba da masana daga ko'ina a duniya kan yadda za su nazarci tekun mai fadin kimanin sikwaya kilomita 106,460,000.

An dai kafa sabuwar cibiyar nazarin harkokin teku ta kasa da kasa a Najeriyar ce kasancewar ta mamba a kungiyar nazarin tekun Atilantika, inda za a rika amfani da na'u'rorin kimiyya da fasaha na zamani.

Onu ya ce, Najeriya ta taka gagarumar rawa a nazarin harkokin teku, idan aka yi la'akari da yankunan da ta yi iyaka ta ruwa, da tasirin da take da shi a fannin tattalin arziki, da kuma yawan jama'a da Allah ya hore mata.

Taken taron kolin dai shi ne "kimiyya da fasaha, da kuma shirin Najeriya da Portugal na yin hadin gwiwa".(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China