170612-Kasar-Sin-na-bada-babbar-gudummawa-a-fannin-yin-tsimin-makamashi-a-duniya-Murtala.m4a
|
A cikin makon tallata tsimin makamashi, kana ranar rage amfani da sinadarai masu gurbata muhalli na bana, an yi bukukuwa daban-daban a wurare da yawa a fadin kasar Sin, wadanda ke da taken "ni kaina zan yi tsimin makamashi, da more rayuwa ba tare da gurbata muhalli ba", da kuma "raya masana'antu ba tare da gurbata muhalli ba".
Baya ga nuna wasu tallace-tallace a fannin kiyaye muhalli da yin tsimin makamashi, za'a yi sauran wasu muhimman ayyuka a fadin kasar, ciki har da tallata tsimin makamashi a makarantu da kamfanoni, gami da unguwanni, da tallata fasahohin zamani na tsimin makamashi, da shigar da kayan tsimin makamashi a kasuwanni, da yin tafiye-tafiye ba tare da gurbata muhalli ba da sauransu, duka dai da zummar fadakar da jama'a kan ilimin neman ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba. Akwai wakilai na wasu kamfanoni, wadanda suka lashi takobin yin tsimin makamashi. Daya daga cikinsu, shi ne mataimakin babban manajan kamfanin Sinopec Group na kasar Sin, Mista Jiao Fangzheng ya bada shawarar cewa:
"Dole ne mu bi ka'idojin tilas na yin tsimin makamashi na kasa, da na kananan hukumomi, da cimma burin yin tsimin makamashi na kowane kamfani, da yin amfani da kayayyaki gami da na'urori masu amfani da makamashi mai tsabta, tare kuma da kafa wani tsari na baiwa mutane kwarin-gwiwa, da ba su kyauta, idan suka ba da gudummawa ta fannin yin tsimin makamashi."
Tun shekaru da dama, kasar Sin ta yi amfani da rage adadin makamashin da ake amfani da shi, in an kwatanta da kowane ma'aunin tattalin arziki na GDP daya, wajen tabbatar da cimma burin raya tattalin arzikin kasa gami da kyautata zaman rayuwar al'umma. A halin yanzu, kasar Sin ta rage yawan dogaronta kan makamashi yayin da take kokarin habaka tattalin arzikinta. Game da wannan batu, mataimakin babban darekta na kwamitin neman ci gaba da yin kwaskwarima na kasar Sin, Mista Zhang Yong ya bayyana cewa:
"Daga shekara ta 2005 zuwa ta 2016, adadin yawan makamashin da ake amfani da shi in an kwatanta da kowane ma'aunin tattalin arziki na GDP daya a kasar Sin, ya ragu da kashi 37. 3 bisa dari. Haka kuma kasar Sin ta yi tsimin ma'adinin kwal har na ton biliyan 1.8, lamarin da ya nuna cewa, kasar Sin ta rage dogaronta kan makamashi mai gurbata muhalli yayin da take kokarin habaka tattalin arziki. Sin ta zama kasa da ta fi bada gudummawa ta fuskar yin tsimin makamashi a duniya daga shekara ta 2005 zuwa ta 2016, wanda hakan ke taka muhimmiyar rawa wajen kiyaye muhalli a fadin duniya baki daya."
Gwamnatin kasar Sin ta riga ta tsara wani buri, wato zuwa shekara ta 2020, adadin yawan makamashin da Sin za ta yi amfani da shi in an kwatanta da kowane ma'aunin tattalin arziki na GDP daya, zai ragu da kashi 15 bisa dari, idan aka kwatanta da na shekara ta 2015.
A halin yanzu, gwamnatin kasar Sin na kokarin tantance ko za a iya cimma wannan buri na tsimin makamashi ko a'a, da kuma kyautata ka'idoji gami da dokokin da suka shafi makamashi da yin tsiminsa. Mista Zhang Yong ya ce, a nan gaba, kasar Sin za ta gaggauta aikin bunkasa kere-kere ba tare da gurbata muhalli ba, da jagorantar yin tsimin makamashi, gami da rage amfani da sinadarai masu gurbata muhalli yayin da ake saye da sayarwa.
Mista Zhang Yong ya nuna cewa,
"Ya kamata mu yi iyakacin kokarin kawo sauye-sauye, da kara kyautata ayyukan masana'antu ba tare da gurbata muhalli ba, da ci gaba da samar da amfani da makamashi mai tsabta a fannin masana'antu. Kazalika, dole ne mu himmatu wajen fadakar da jama'a kan yin saye da sayarwa ba tare da gurbata muhalli ba, da yin kira da a kara tsimin kudi a fannonin da suka jibanci tufafi, da abinci, da zamantakewa, da tafiye-tafiye, da bulaguro da sauransu. Ya zama dole mu kaucewa kashe kudaden da suka wuce kima, da yin sama da fadi da kudade, mu kuma yayata wani ra'ayi ko al'ada, ta kashe kudi ta hanyar da ta dace."(Murtala Zhang)