in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rwanda ta kaddamar da tashar juya bolar kayayyakin laturoni ta farko
2017-12-05 12:03:12 cri

Rwanda ta kaddamar da wata tashar juya bolar kayayyakin laturoni na farko, wanda ke da nufin kare kasar daga hadduran muhalli da ba da gudunmuwa ga raya tattalin arziki da samar da aikin yi a bangaren kare muhalli.

Tashar dake da mazauni a gundumar Bugesera na lardin gabashin kasar, zai samar da dawwamammiyar mafita ga bolar kayayyakin laturoni yayin da zai kare mummunan tasirinsa ga lafiyar bil adama da muhalli.

Yayin taron kaddamarwar, ministan muhalli na kasar Vincent Biruta, ya ce tashar shaida ce ga burin Rwanda na rayawa da samar da muhalli mai tsafta domin ci gabanta.

Ya ce, tashar za ta rika juya bular kayayyakin laturoni dake da hadari ga muhalli a kasar.

A cewar Ministan, Baya ga kare muhalli, ana sa ran tashar za ta ba gwamnati damar adana biliyoyin kudin Franc, da zarar an kwashe tare da juya bolar laturoni domin sake amfani da shi.

Shi kuwa ministan ciniki da masana'antu na kasar Vincent Munyeshyaka cewa ya yi, tashar za ta taimakawa kasar alkinta muhalli, yayin da za ta samar da ayyukan yi tare kuma da rage barazanar hadarrun sinadaran laturoni dake da illa ga lafiyar bil'adama da muhalli.

Da farko a jiyan, Rwanda ta kaddamar da makon raya muhalli, wanda ya kunshi jerin shirye-shirye da zai hada masu ruwa da tsaki, inda za su yi musayar ra'ayoyi kan batutuwan raya muhalli mai tsafta da tunkarar yanayi. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China