in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rwanda za ta bullo da shirin wayar da kai game da safarar bil adama
2017-02-07 09:14:11 cri

Karamin minista mai kula da harkokin da suka shafi tsarin mulki da harkokin shari'a a kasar Rwanda Evode Uwizeyimana, ya ce yanzu haka ana shirin bullo da wani tsari na musamman, domin wayar da kan al'ummar Rwanda game da hadarin dake tattare da safarar bil adama.

Mr. Uwizeyimana ya shaidawa manema labarai cewa, ma'aikatar shari'ar kasar Rwanda na tsara shirin wayar da kan jama'a, mai kunshe da fadakarwa game da fadin wannan matsala, da tasirin ta, da ma mummunan hadarin dake tattare da ita.

A bara dai kasar Amurka ta fidda wani rahoto, wanda ya sanya kasar ta Rwanda a matsayin kasar da ake yawan aikata wannan mummunar sana'a ta safarar bil'adama, kana rahoton ya ce, wasu kasashen na daman ma na amfani da ita a matsayin zango na aikata wannan laifi, lamarin dake jefa mata da kananan yara da dama cikin kangin bauta da karuwanci.

To sai dai kuma gwamnatin Rwandan ta musanta wannan zargi, tana mai cewa, rahoton na Amurka ya wuce gona da iri, domin kuwa ya kambama girman wannan matsala fiye da kima.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China