Ma'aikatar samar da gidaje da raya birane da karkara ta kasar Sin ta ce ya zuwa shekarar 2020, dukkan biranen kasar za su fara aikin tantance shara.
Ministan ma'aikatar Wang Menghui ne ya bayyana haka yayin wani taro da ya gudana a birnin Xiamen na lardin Fujian, inda ya ce ya zuwa 2020, dole ne biranen su dauki dokokin da suka dace tare da ingantattun dabarun tantance shara.
Wang Menghui ya kara da cewa, ya kamata dukkan hukumomin gwamnati su rika tantance shara ya zuwa 2020, bayan biranen 46 da za a fara gwajin shirin da su, sun samar da tsarin da za a yi amfani da shi.
Ya jaddada bukatar gaggauta samar da dokoki da za su mara baya ga tsarin, tare da kirkiro shirye-shiryen da za su karfafa gwiwar aiwatar da shirin a fadin kasar.
Ya kuma yi kira da a kara yunkurin inganta aikin tattara shara da kwashewa da kuma kawar da shi a yankunan karkara.
Wannan tsari na zuwa ne a daidai lokacin da biranen kasar Sin ke fuskantar matsalar tarin shara, yayin da mazauna karkara kuma ke adawa da hanyoyin kawar da shara na zamani. (Fa'iza Mustapha)