Li wanda ya bayyana hakan yayin da yake gabatar da jawabi a taron dandalin tattalin arziki da cinikayya na Sin da kasashen tsakiya da gabashin Turai karo na bakwai a birnin Budapest na kasar Hungry, ya kuma sanar da kafa kungiyar hadin kan bankunan Sin da hadakar kungiyar kasashen na CEEC da kuma kashi da biyu da gidauniyar hadin gwiwar Sin da kasashen yankin tsakiya da gabashin Turai.
Mr Li ya ce bankin ci gaba na kasar Sin zai samar da kimanin euro biliyan biyu, kwatankwacin dala biliyan 2.4 a matsayin kudin rance ga kungiyar da aka kafa.
A halin da ake ciki kuma, firaministan na kasar Sin ya bayyana cewa, kashi na biyu na gidauniyar hadin gwiwar zuba jarin da za ta kai dala biliyan 1, za a zuba shi ne a yankin tsakiya da gabashin Turai.(Ibrahim)