in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An ce rashin kyawun yanayi na tasiri ga aikin kai samame kan Boko Haram
2017-07-28 09:31:37 cri

Rundunar sojin saman Nijeriya, ta ce rashin kyawun yanayi na mummunan tasiri a kan ayyukan soji, a yaki da suke da mayakan Boko Haram a yankin arewa maso gabashin Nijeriya.

Kwamnadan rundunar karkashin shirin 'Operation Lafiya Dole' Air Commodore Tajudeen Oladele ne ya sanar da haka jiya a birnin Yolan jihar Adamawa, lokacin da yake wa manema labarai bayani game da ayyukan rundunar tsakanin watannin Afrilu da Yuni.

Air Commodore Oladele, ya ce babban kalubalen da ayyukan soji ta sama ke fuskanta a wannan lokaci shi ne, rashin kyawun yanayi, yana mai cewa, ruwan sama da cida na kawo cikas ga ayyukan na soji.

Ya ce, akwai wasu lokuta da ake jinkirtawa ko soke tashin jirgi saboda yanayin.

Sai dai ya ce, duk da kalubalen, an gudanar da muhimman ayyuka a cikin wadancan watannin.

Kwamandan ya ce, jimilar samame 821 aka kai cikin sa'o'i 1,256 da minti 9 na shawagin jirgi.

Air Commodore Tajuddeen Oladele ya kuma jadadda kudurin rundunar na ci gaba da yakar Boko Haram, tare da ba da goyon bayan ga ayyukan sojin kasa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China