171130-Ghana-ta-samu-matsayi-na-51-a-jadawalin-hukumar-FIFA-zainab.m4a
|
Duk da kasancewa kungiyar wasan Black Stars, ta samu maki 6 inda hakan ya bata damar kara adadin makinta daga jimmalar maki 651 zuwa 657, sai dai ta sauka kasa daga matsayi na 9 a cikin jadawalin jerin sunayen da aka fitar na nahiyar Afrika a cikin wannan wata.
Ghana ta tsallake matsayi guda ne bayan data tashi kunnen doki da Masar a zagayen karshe na gasar share fage na FIFA, wanda aka buga a katafaren filin wasan Cape Coast wanda kasar Sin ta gina.
Senegal ta daga zuwa matsayi na 23, wanda shine matsayi na koli da kasar ta taba kaiwa a wasannin kasa da kasa, tun bayan matsayin farko data taba samu a gasar cin kofin duniya na shekarar 2002.
A halin yanzu kasashen yammacin Afrika sune a bisa matsayin koli a tsakanin kasashen nahiyar ta Afrika, inda suka sha gaban takwarorinsu na Masar da Tunisiya a gasar share fagen cin kofin duniya wanda za'a buga a Rasha a shekarar 2018.
Ghana bata samu damar tsallakewa a gasar ta FIFA ta 2018 ta kasar Rasha ba, sai dai a halin yanzu, ta samu kwarin gwawi na shiga gasar cin kofin kasashen Afrika (AFCON) a shekarar 2019 wanda za'a cigaba da fafatawa a gasar share fagen a watan Maris.(Ahmad Fagam)