in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar FIFA na aiwatar da wani shiri na bunkasa kwallon kafa a Namibia
2017-11-29 09:51:35 cri
Hukumar kwallon kafa ta kasa da kasa FIFA, da hadin gwiwar hukumar kwallon kafar kasar Namibia (NFA), na gudanar da wani shiri na bunkasa kwallon kafa a Namibia, a wani mataki na bunkasa wasan, da kuma amfani da shi wajen karfafa hanyoyin kiwon lafiya.

Cikin wata sanarwa da aka fitar, masani a fannin samar da kayayyakin bukata na wasan kwallon kafa Ian McClements, ya bayyana irin nasarar da wannan shiri ke samu. Yana mai cewa makarantu da dama sun amfana daga wannan shiri.

Mr. McClements ya ziyarci Namibia a baya bayan nan, domin duba ci gaban da ake samu a aikin gyaran wasu fiyalen wasa dake Khomas da Ohangwena, filayen da aka kaddamar da fara amfani da su a watan Fabarairun farkon wannan shekara.

A cewar McClements, burin wannan shiri ya hada da baiwa makarantun kasar 23, tare da wata cibiyar koyar da sana'oi dake kasar damar samun filayen wasa masu nagarta, wanda hakan zai baiwa matasa damar samun horo na kwallon kafa tun daga tushe.

Bugu da kari FIFA na fatan amfani da wasan kwallon kafa wajen gabatarwa matasa damar fahimtar batutuwa na lafiya, ciki hadda batun yaki da cutar HIV/AIDS, da kuma samar da kayan wasa, baya ga baiwa yara damar motsa jiki yadda ya kamata.

A wani ci gaban kuma, hukumar ta FIFA da hadin gwiwar hukumar wasanni ta kasar Jamus, sun samar da kayan wasa, tare da horas da masu bada horo, da alkalan wasa, da ma jami'an dake lura da shirya gasanni a kasar.

McClements ya dade yana sanya ido a fannin duba nagartar filayen wasa cikin tsawon shekaru 26, ya kuma ziyarci wurare 15 a arewacin kasar Namibia. Kaza lika jami'in ya tsara filayen wasa 5 a nahiyar Afirka, ciki hadda Zambia, da Afirka ta kudu, da Botswana, da Morocco, da kuma Tanzania.

Ya kuma kasance cikin wadanda suka lura da ginin filayen wasa a Afirka ta kudu, gabanin gasar cin kofin duniya da aka buga a kasar a shekarar 2010. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China