in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Angola ta lashe dukkanin wasannin ta na rukuni a share fagen buga gasar FIBA ta 2019
2017-11-29 09:48:33 cri
Kasar Angola ta kammala wasannin ta na neman gurbin buga gasar kwallon Kwando ta kasa da kasa PIBA a zagayen farko, gabanin gasar da za a buga a shekarar 2019 a kasar Sin.

Angola dai ta kammala wasan ta na karshe da janhuriyar dimokaradiyyar Congo da maki 73-64, yayin wasan rukunin C da aka buga a birnin Luanda a ranar lahadin karshen mako.

A wasan na neman gurbi zagaye na farko, Masar ce ta zamo ta biyu bayan ta doke Morocco.

Ana dai sa ran kungiyoyin dake neman gurbin buga wannan gasa za su fara zagaye na biyu, na wasanni daga watan Yunin shekara mai zuwa a kasar Masar.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China