in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijeriya na bincike kan manyan jami'ai 2 game da cin hanci da rashawa
2017-04-20 09:43:43 cri

Gwamnatin Nijeriya ta ce, za a gudanar da bincike kan zargin cin hanci da almudahana da ake wa wasu manyan jami'anta biyu.

A jiya Laraba ne shugaban kasar Muhammadu Buhari ya ba da umarnin dakatar da sakataren gwamnatin tarayya David Lawal da darakta janar na hukumar liken asiri ta kasar NIA Ayo Oke.

Babban mashawarcin shugaban kasar kan harkokin yada labarai Femi Adesina ya bayyana jiya a Abuja, babban birnin kasar cewa, an dakatar da jami'an har zuwa lokacin da za a samu sakamakon bincike kan zarge-zargen da ake musu.

Shugaban kasar ya kafa kwamiti mai kunshe da mutane uku da za su aiwatar da binciken karkashin jagorancin mataimakinsa, inda kwamitin zai mika masa rahotonsa cikin kwanaki 14.

Za a binciki sakataren gwamnatin ne kan zargin take dokoki da ka'idoji wajen ba da kwangiloli karkashin shirin fadar shugaban kasa na farfado da yankin arewa maso gabashin kasar (PINE).

Yayin da aka dakatar da Ayo Oke domin gudanar da cikakken bincike kan makudan kudaden ketare da na gida da hukumar EFCC mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasar tu'annuti ta gano a wani gida a jihar Lagos, kudaden da NIA ta yi ikirarin na ta ne. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China