in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijeriya na karfafa tsarin amfani da masu kai tsegumi wajen yaki da cin hanci
2017-04-20 09:11:30 cri

Gwamnatin Nijeriya ta lashi takobin kara kaimi wajen karfafa tsarin amfani da masu kai tsegumi a yaki da take da cin hanci a kasar.

Wata sanarwa da kakakin shugaban kasar Garba Shehu ya fitar jiya Laraba ta ce, wannan mataki ya biyo bayan irin nasarori da ake samu wajen yaki da cin hanci da rashawa.

Garba Shehu ya ce, yadda 'yan Nijeriya suke ba da hadin kai ga tsarin na kai tsegumin, ya karfafa shirin gwamnatin Muhammadu Buhari na yaki da cin hanci, a don haka ne gwamnati ke duba hanyoyin inganta tsarin.

Ya kara da cewa, gwamnatin na duba yiyuwar inganta tsarin ta hanyar sanyata karkashin kwamiti mai ba da shawara ga shugaban kasa kan yaki da cin hanci ko kuma wata hukuma, domin kara wa tsarin karfi, ta yadda zai zama muhimmin batu ga kasar.

Garba Shehu ya kuma yabawa karsashi da kishi irin na 'yan Nijeriya, kan yadda suke ba tsarin goyon baya, wanda ke da nufin bankado dukiyar da aka yi sama da fadi da su.

A baya-bayan nan ne, jami'an hukumar yaki da cin hanci da rashawa na kasar suka gano dala miliyan 43.4 a wani gida dake unguwar Ikoyi a jihar Lagos. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China