in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kori wani janar na Libya daga aiki bisa barazanar da ya yi na kai hari Alkahira
2017-11-06 10:15:54 cri

Gwamnatin kasar Libya ta kori wani babban jami'in sojinta daga aiki, wanda ya yi barazanar kai hari kan fadar shugaban kasar Masar da ofisoshin gwamnati dake birnin Alkahira.

Wani jami'in sashen shigar da kara na rundunar sojin kasar, ya ce bincike ya gano cewa, janar Mohammed Gneidi, jami'in sashen tattara bayanan sirri da ya fito daga yankin Misurata na kasar, ya take dokokin aikin soji ta hanyar zantawa da kafafen yada labarai kafin a ba shi izini, tare kuma da yin barazanar kai hari kan fadar shugaban kasar Masar, yana mai cewa, abubuwa ne da ba za a aminta da su ba.

Jami'in ya ce, firaministan kasar Fayez Serraj ya yi amfani da sakamakon binciken da kuma kin bayyanar janar Gneidi a gaban kotun rundunar, wajen yanke shawarar korarsa daga aiki da ma rundunar baki daya.

Janar Mohammed Gneidi ya soki hukumomin Masar a lokacin da yake ganawa da wata tashar watsa labarai ta kasar Libya a ranar Asabar da ta gabata, game da luguden wuta da wani jirgin yakin da ba san inda ya fito ba ya yi a birnin Derna kwanakin da suka gabata, inda ya zargi rundunar sojin saman Masar da kai harin.

Har ila yau, janar Gneidi ya yi barazanar mai da martani ga harin da ya ce Masar ta kai wa kasarsa, ta hanyar kai hari kan gine-ginen gwamnatin Masar, ciki har da fadar shugaban kasar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China