Hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Borno dake arewa maso gabashin Nijeriya, ta ce mutane 4 sun mutu sanadiyyar wani hari da kungiyar 'yan tada kayar baya ta Boko Haram ta kai wani gari dake kusa da Maiduguri, babban birnin jihar.
Shugaban hukumar Bello Dabatta ya ce, ana zargin wasu mata 4 'yan kunar bakin wake da kai hari kauyen Mandirari dake karamar hukumar Konduga, wanda ba shi da nisa da birnin Maiduguri.
A cewarsa, fararen hula hudu ne suka mutu, yayin da babu takamaimai adadin wadanda suka jikkata.
Duk da ayyukan soji, yankin arewa maso gabashin Nijeriya na ci gaba da fuskantar muggan hare-hare daga kungiyar Boko Haram, musamman a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
Ko cikin watan da ya gabata, birnin Maiduguri ya yi fama da hare-hare a lokacin bukukuwan karamar sallah. (Fa'iza Mustapha)