in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Asibitin tafi da gidanka na jirgin ruwan kasar Sin ya kammala aikin ba da agaji a Tanzania
2017-11-27 09:13:18 cri

Shugaban kasar Tanzania John Magufuli ya godewa likitoci Sinawa da suka duba marasa lafiya 6,000 a asibitin tafi da gidanka na jirgin ruwan kasar Sin wato Peace Ark, yayin zaman kwanaki 8 da ya yi birnin Dar es Salaam, cibiyar kasuwancin kasar.

John Magufuli ya kai wa jirgin Peace Ark ziyara ne a jiya Lahadi, inda ya yi ban kwana da likitoci da sojojin ruwan na kasar Sin.

Jirgin ya isa Dar es Salaam ne a ranar 19 ga wannan wata, wanda shi ne zuwa na biyu da ya yi kasar cikin shekaru 7 domin aikin kula da lafiya kyauta ga mazauna yankin.

Yayin zamansa a Tanzania, likitoci Sinawa sun duba jimilar marasa lafiya 6,441.

Tsakanin shekarar 2010 zuwa 2015, jirgin Peace Ark ya ziyarci yankin Asiya da Afrika da Amurka da Oceania. Inda ya duba marasa lafiya kyauta da adadinsu ya kai kimanin 120,000 daga kasashe da yankuna 29.

A rangadin na wannan karon, Peace Ark ya je kasashen Djibouti da Gabon da Saliyo da Jamhuriyar Congo da Angola da Mozambique kafin tsayawarsa a Tanzania. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China