in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jirgin ruwan agajin kiwon lafiya na kasar Sin Peace Ark ya isa Tanzania
2017-11-20 10:32:03 cri
Jirgin ruwan ba da taimakon kiwon lafiya na kasar Sin wato Peace Ark da safiyar ranar Lahadi ya isa Dar es Salaam, babban birnin kasar Tanzaniya, domin fara aikin taimakon kula da lafiyar jama'ar kasar har na tsawon kwanaki 8.

Wannan shi ne karo na biyu cikin shekaru 7 da jirgin ruwan Peace Ark, ya ziyarci kasar Tanzaniyar domin ba da taimakon kula da lafiyar jama'ar kasar.

A bikin da aka gudanar na maraba da zuwan jirgin a tashar ruwan Dar es Salaam, babban kwamandan tawagar likitocin Peace Ark Guan Bailin, ya bayyana cewa, jami'an kiwon lafiyar na kasar Sin za su gudanar da aikin kula da lafiyar al'ummar kasar a kyauta, da bada taimakon jin kan al'umma, kana da bada horo kan kiwon lafiya da kuma karfafa kyakkyawar abokantaka a tsakanin kwararrun kasashen Sin da Tanzania.

Babban kwamandan sojojin ruwa na kasar Tanzania Richard Mutayoba Makanzo, ya godewa kasar Sin bisa sake tura jirgin ruwan Peace Ark zuwa Tanzaniyan.

Ya ce, kasar Sin ta taimakawa kasar Tanzaniya a bangarori da dama. Daya daga cikin manyan taimakon da ta samar shi ne na gina layin dogo na Tazara, wanda ya hada kasashen Tanzania da Zambia.

Tsakanin shekarar 2010 zuwa 2015, jirgin ruwan Peace Ark ya ziyarci sassan nahiyoyin Asiya, Afrika, Amurka da Oceania. Kimanin kasashe da yankuna 29 ya ziyarta, inda ya taimakawa mutane kimanin 120,000 ta hanyar duba lafiyarsu a kyauta da kuma bada agaji ga al'umma. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China