in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jirgin ruwan Peace Ark ya taimakawa majinyata da dama a Tanzania
2017-11-22 10:58:21 cri

Jiya ne rana ta uku da jirgin ruwan dake ba da jinya kyauta na kasar Sin mai suna na Peace Ark ya iso kasar Tanzania dake gabashin Afirka, inda ya taimakawa majinyata da dama a Dar es salaam, birnin da ta girma a kasar.

Ya zuwa tsakar ranar jiya, ma'aikatan dake aikin ba da tallafin jinyar sun ba da hidimar jinya ga mutane 2115 a kasar ta Tanzania, tare kuma da duba lafiyar mutane 1483 ta daukar hoton sassan jiki na musamman, binciken bugun zuciya da dai sauransu, baya ga wasu na'urorin kiwon lafiya 5 da suka gyara, kana yiwa a mutane 4 aikin tiyata. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China