Cikin shekaru da dama tsakanin 2010 da 2015, jirgin Peace Ark ya kai ziyara nahiyar Asia da Afrika da Amurka da yankin Oceania, inda ya duba lafiya kyauta ga jimilar kasashe da yankuna 29 da mutane 120,000.
Jirgin na da tsawon mitoci 178 da fadin muraba'in mita 4,000. Kuma ya kunshi dakunan fida 8 da dakunan ganin likita 7 da gadaje 300.
Har ila yau, jirgin na da jimilar ma'aikatan lafiya 115, galibinsu daga jami'ar kiwon lafiya ta sojojin ruwa, inda kashi 60 daga cikinsu suka kasance manyan jami'ai.
Peace Ark ya isa Djibouti ne a ranar Laraba da ta gabata, kuma ana sa ran zai kwashe kwanaki 9 ya na aiki a kasar, inda daga nan zai wuce kasashen Saliyo da Gabon da Tanzania da sauran wasu kasashe domin bada tallafin jin kai da kiwon lafiya kyauta. (Fa'iza Mustapha)