Bayanai na cewa, shugabanni da kusoshin gwamnatocin kasashen Afirka ta Kudu, Angola, Tanzania da Zambia ne za su halarci taron. Yanzu haka shugaban kungiyar SADC na wannan karo, kuma shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya tura manzon musamman zuwa kasar Zimbabwe don ganawa da bangarorin da abin ya shafa.
Zuma ya jaddada cewa, kungiyar SADC ba ta goyon bayan duk wani salo na juyin mulkin da ya saba kundin tsarin mulki, ya ce, kungiyar SADC, kungiya ce mai neman zaman lafiya da kwanciyar hankali da kare muradun 'yan kasar, kuma kasar Zimbabwe muhimmin memban kungiyar ce. (Zainab)