Bayan bikin, Xi da Boungnang sun ziyarci babban ginin asibitin, inda suka gana da ma'aikatan jinya a sashin kula da ido na kasar Sin wadanda suka je kasar Laos don bada taimako. Shugaba Xi ya jinjinawa wadannan ma'aikatan jinya saboda matukar kokarin da suka yi wajen karfafa dankon zumunci tsakanin jama'ar kasashen biyu.
Xi Jinping ya kuma nuna cewa, ya kamata a kara maida hankali kan kyautata zaman rayuwar al'umma, yayin da ake gudanar da ayyukan hadin-gwiwa tsakanin Sin da Laos, ta yadda al'umma za su ci alfanu.
Asibitin Mahosot, asibiti ne wanda kasar Sin ta bada tallafi wajen ginawa a kasar Laos, kuma za'a fara amfani da shi a shekara ta 2021.(Murtala Zhang)