Shugabannin kasashen Sin da Vietnam, sun amince da daukar matakai na fafada hadin gwiwa dake tsakanin kasashen su a sabon yanayin da suke ciki.
Shugaba Xi Jinping na kasar Sin, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin koli na JKS, da babban sakataren kwamitin koli na jam'iyyar kwaminis ta kasar Vietnam CPV Mr. Nguyen Phu Trong ne suka amince da hakan, yayin tattaunawar da suka gudanar, a ziyarar da shugaba Xi ya gudanar a Vietnam.
Jagororin biyu dai sun amince da fadada kawance, tare da bunkasa fahimtar juna, matakin da suka yi amannar zai haifar da tarin moriya ga al'ummun su.(Saminu)