in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ghana ta dauki matakan kyautata harkokin kasuwanci
2017-06-22 09:48:29 cri

Shugaban kasar Ghana Nana Dankwa Afuko-Addo ya ce, gwamnatinsa ta dauki wasu matakai na saukakawa tare da kyautata harkokin kasuwanci.

Matakan sun hada da inganta bangarori masu zaman kansu da tsarin kudi da zai daidaita takardar kudin kasar da kuma rage karbar rance, baya ga rage yawan haraji.

Nana Akufo-Addo wanda ya bayyana haka jiya a birnin Accra, lokacin da yake jawabi ga kwamitin din din din kan harkokin waje, na kungiyar kawancen jam'iyyun siyasa ta kasa da kasa wato IDU, ya ce tuni matakan suka fara rage yawan kudin da ake kashewa na yin kasuwanci tare da karkatar da akalar tattalin arziki daga kan haraji zuwa sarrafa kayayyaki.

Shugaban na Ghana ya kara da cewa, manufar gwamnatinsa ita ce kara inganta yanayin kasuwanci da kuma mayar da Ghana wajen da za a iya gudanar da kasuwanci cikin sauki ta hanyar yin hada-hadar kudi ba tare da amfani da takardu ba a gabobin ruwa da kuma janye dukkan shingayen kwastam na cikin gida daga farkon watan Satumba. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China