in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin mai na Brazil zai daina aiki a Najeriya
2017-11-08 09:38:21 cri

Wani katafaren kamfanin mai na kasar Brazil Petrobras ya sanar da cewa, zai janye reshensa a Najeriya a wani mataki na shirinsa na janye hannayen jari.

A wata sanarwa da aka fitar, Petrobras ya bayyana cewa, reshen kamfanin man dake Najeriya, wato Petrobras Oil & Gas B.V. (POGBV), tuni an riga an sayar da shi. A halin da ake ciki, kamfanin na Petrobras yana da kashi 50 cikin 100 ne na jarin, kamfanin BTG Pactual E&P B.V. yana da kashi 40 bisa 100, sai kuma kamfanin Helios Investment Partners wanda ke da ragowar kashi 10 bisa 100.

Shi dai kamfanin na Petrobras yana fuskantar tuhume-tuhume bisa zargin aikata rashawa, tun bayan da aka zargi manyan jami'an gudanarwar kamfanin, da wasu abokan hulda da kuma wasu jami'an gwamnatin kasar da zargin almundahanar wasu biliyoyin daloli a cikin shekaru 10.

Reshen kamfanin dake kasar yana gudanar da aiki a wasu yankunan Najeriya biyu masu arzikin mai, wato Akpo da Agbami, wanda katafaren kamfanin man nan na kasar Faransa Total, yake samar da kimanin gangar danyen mai dubu 368 a ko wace rana.

POGBV ya adana mai da yawansa ya kai gangan miliyan 204, kuma a halin yanzu yana iya samar da ganga dubu 48 a ko wace rana, kana ana sa ran kamfanin zai dinga samar da gangar danyen mai dubu 75 a kullum nan da shekarar 2019.

A kokarin kamfanin na warware matsalar dunbun basukan da yake fama da ita, da kuma maido da martabarsa, kamfanin man na Petrobras yana kokarin cefanar da hannun jarinsa domin tattara kimanin dala biliyan 21 nan da karshen shekarar 2018.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China