Yanzu haka dai mahaukaciyar guguwar ta yi barna a Houston na kasar Amurka, inda manyan matatun man kasar suke, da kuma wasu sassan jihar Taxes.
Mummunan yanayi ya tilasatwa matatun man dakatar da ayyukansu. Alkalumna na nuna cewa, mahaukaciyar guguwar ta sa matatun man dakatar da sama da kashi 20 cikin 100 na yawan man da suke tacewa a fadin kasar.
A farkon wannan makon, farashin mai ya fadi kasa warwas, yayin da rufe matatun man ka iya tilastawa Amurka rage bukatunta na danyen mai. (Ibrahim)