in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An damke wani mayakin Boko Haram a Abujan Najeriya
2017-07-25 09:27:57 cri

Yan sandan Najeriya sun sanar da cewa, sun kama wani mamba na kungiyar Boko Haram, wanda ake zarginsa da yunkurin kaddamar da mummunan harin ta'addanci a Abuja, babban birnin kasar.

Mutumin mai shekaru 20 da haihuwa mai suna Seth Yakubu, an kama shi ne a Gwagwalada, dake wajen birnin na Abuja a ranar Lahadi.

Musa Kimo, shi ne shugaban 'yan sandan birnin Abuja ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, wanda ake zargin ya amince cewar, shi mamba ne na kungiyar Boko Haram, kuma ya kauro Abuja ne bayan da ya tsere daga sansanin da suke samun horo a dajin Sambisa bayan da dakarun tsaron Najeriya suka fatattaki mayakan daga dajin.

A cewar Kimo, wanda ake zargin ya tabbatar da cewa, shi ne kwamanda na biyu na sashen kungiyar da suke jagoranta, kuma a cewarsa ya sha jagorantar hare haren ta'addanci masu yawa da kungiyar ta kaddamar.

Masu gudanar da bincike kan 'dan kungiyar ta Boko Haram sun ce, wanda ake zargin ya bayyana musu cewa, an ja hankalinsa ya shiga kungiyar ne a watan Oktoban 2016, inda aka yi masa alkawarin cewa, za'a ba shi aiki a rundunar sojin Najeriya.

Kimo ya ce, wanda ake zargin, za'a gurfanar da shi ne a gaban kotu da zarar 'yan sandan sun kammala bincikensu.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China