in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD na fatan ganin Amurka ta dage haramcin shiga kasar na wucin gadi da ta sanya wa 'yan gudun hijira
2017-02-01 13:07:31 cri
A jiya Talata ne MDD ta ce tana fatan ganin Amurka ta dage haramcin shiga kasar na wucin gadi da ta sanyawa 'yan gudun hihjira nan bada dadewa ba.

Dubban masu zanga-zanga ne suka yi jerin gwano a gaban fadar White House dake Washington D.C a ranar Lahadi da ta gabata, yayin da ake ci gaba da zanga- zanga a filayen jirgin saman kasar sama da talatin, bayan da shugaban Kasar Donald Trump ya rattaba hannu kan wani takardar umarni na haramtawa 'yan gudun hijira da kuma 'yan wasu kasashe bakwai na yankin gabas ta tsakiya da arewacin nahiyar Afrika shiga Amurka.

Karkashin wannan takardar umarni, an dakatar da shigar 'yan gudun hijira Amurka na tsawon kwanaki dari da ashirin, yayin da aka hana mazauna kasasshen dake da alaka da ayyukan ta'addanci shiga kasar na tsawon kwanaki casa'in. kasashen sun hada da Iraqi da Syria da Iran da Sudan da Libya da Somalia da kuma Yemen.

Da farko, a jiya Talata, Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya fitar da wata sanarwa akan hanyarsa ta dawowa daga Kasar habasha, inda ya ce bai kamata duk wata kasa dake kokarin kare iyakarta daga kwararar yan gudun hijira ta yi hakan bisa dalilai na banbancin kabila, addini ko asali ba.

Yayin da yake halartar taron kungiyar AU a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha a ranar Litinin da ta gabata, Sakatare Janar din ya yabawa kasashen Afrika, game da yadda suka budewa 'yan gudun hijira dake tserewa daga kasashensu sanadiyyar tashe-tashen hankula iyakokinsu, a daidai lokacin da sauran sassan duniya ciki har da kasashen yamma da suka ci gaba, ke rufe iyakokinsu ko kuma gina katanga.( Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China