in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An tasa keyar bakin haure 7,000 daga Sabratha na Libya
2017-10-16 09:10:24 cri

Hukumar yaki da kungiyar IS a Libya, ta ce kawo yanzu ta tasa keyar bakin haure 7,428, tun bayan da ta fara aiki a birnin Sabratha dake yammacin kasar.

Wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce a wani bangare na aikin ofishin yaki da shige da fice ba bisa ka'ida ba dake gudana da hadin gwiwar hukumar yaki da kungiyar IS, na ci gaba da farautar matsugunan bakin haure a birnin.

Shugaban ofishin yaki da shige da ficen ba bisa ka'ida ba a Sabratha Bassam al-Gharabli, ya ce an samu sama da bakin haure 3,000 a cibiyoyin da ake tsare su, wadanda ke shirin tsallake Libya don isa Turai cikin kwale-kwale, a daidai lokacin da hukumar yaki da kungiyar IS ta fara aiki a birnin tare da cin nasara a kan kungiyoyi masu dauke da makamai.

An shafe makonni ana gwabza fada tsakanin dakarun hukumar da kungiyoyin adawa dake da alaka da rundunar sojin birnin, al'amarin da ya yi sanadin mutuwa da jikkatar daruruwan mutane. An kawo karshen fadan ne bayan da dakarun hukumar yaki da IS suka kwace iko da garin tare da cin nasara a kan kungiyoyin.

A makon da ya gabata ne hukumar kula da baki ta MDD ta bayyana damuwa game da tasirin fadan a kan bakin haure dake tsare a birnin. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China