Hukumar zabe mai zaman kanta ta jamhuriyar demokaradiyyar Congo DRC (CENI) ta ayyana ranar 23 ga watan Disambar shekarar 2018 a matsayin ranar da za ta gudanar da zaben shugaban kasar.
Shugaban hukumar zaben kasar CENI, Corneille Nangaa, ya bayyana a Kinshasa, babban birnin kasar cewa, za'a gudanar da zaben shugaban kasar ne tare da na 'yan majalisun dokoki da kuma shugabannin larduna a lokaci guda.
Nangaa ya ce, an hada zabukan kasar a lokaci guda ne domin takaita kashe kudade a tsarin zaben kasar.
Shugaban na CENI ya bayyana cewa, za'a rantsar da shugaban kasar da za a zaba a ranar 13 ga watan Janairun shekarar 2019.
Manyan abokan hamayyar dake kalubalantar shugaban kasar mai ci Joseph Kabila, sun yi watsi da sabon jadawalin gudanar da zaben kasar.(Ahmad Fagam)