in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a dage zaben shugaban kasar DRC zuwa Afrilun 2018
2016-10-19 10:25:24 cri

A ranar Litinin mahalarta tattaunawar siyasa a Kinshasa, babban birnin kasar jamhuriyar demokuradiyar Congo DRC sun rattaba hannu kan yarjejeniyar siyasa ta karshe wacce za ta dage shirya zaben shugaban kasar har zuwa tsakiyar watan Afrilun shekarar 2018 a karkashin jagorancin mai shiga tsakani na kungiyar tarayyar Afrika AU.

Vital Kamerhe, mai shiga tsakani na biyu na bangaren 'yan adawa a wannan tattaunawa, ya bayyana cewa, za a kawo karshen aikin sake duba rijistan zabe a ranar 31 ga watan Yulin shekarar 2017, ajiye takardun takara na zaben shugaban kasa da na 'yan majalisu, sannan da zaben kananan hukumomi a cikin watan Oktoban shekarar 2017, daga karshe za a shirya zabuka uku a ranar 24 ga watan Afrilun shekarar 2018.

Joseph Kabila, shugaban kasar mai ci yanzu, na kan karagar mulki tun a shekarar 2001, bayan juyin mulkin da ya halaka ma'aifinsa Lauren Desire Kabila, tsohon shugaban DRC-Congo.

Wa'adinsa na biyu da wa'adi na karshe bisa kundin tsarin mulkin kasar zai kare a wannan shekara, amma rashin gudanar da zabuka cikin lokutan da aka tsaida, dalilin haka Joseph Kabila zai tsaya shugaban kasar har zuwa lokacin da za a gudanar da zabuka masu zuwa, a cewar yarjejeniyar siyasa da aka cimma a yayin wannan tattaunawa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China