in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar sojin Burundi ta karyata arangama da ake cewa ta yi da sojojin DRC
2016-12-30 10:28:11 cri

Kakakin rundunar sojojin kasar Burundi kanar Gaspard Baratuza, ya karyata wasu bayanai da ake yadawa ta kafofin sada zumunta, wadanda ke cewa, sojojin Burundi sun yi arangama da takwarorin su na janhuriyar dimokaradiyyar Congo DRC, matakin da ya kai ga hallaka sojojin Burundin su 10.

Baratuza wanda ya musanta wannan batu yayin wani taron manema labarai a jiya Alhamis, ya ce ko alama wannan batu ba gaskiya ba ne. Ya ce, dauki ba dadin da aka yi, ya faru ne tsakanin wasu bata gari da suka tsere daga Burundi sanye da kayan soji, bayan yunkurin juyin mulkin ranar 13 ga watan Mayun shekarar 2015 wanda bai yi nasara ba, da dakarun kasar Congo ko FARDC a takaice.

Sannan sassan biyu dai sun yi musayar wutar ne a Kiliba dake Congon, tsakanin ranekun 21 da 22 ga watan nan na Disamba, an kuma ce wasu daga sojojin sun rasa rayukan su.

Sai dai a martanin sa Mr. Baratuza ya ce, Burundi da janhuriyar dimokaradiyyar Congo, na da kyakkyawar mu'amalar diflomasiyya, kuma rundunonin sojin suna hadin gwiwa yadda ya kamata, ba tare da wata matsala ba. Bisa hakan ne kanar Baratuza ya bukaci al'umma da su yi watsi da wannan labari maras tushe.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China