in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta karbi bakuncin 'yan gudun hijira dubu 600 daga Sudan ta Kudu
2017-04-17 10:29:48 cri

A jiya Lahadi gwamnatin kasar Sudan ta sanar da cewa, ta karbi bakuncin 'yan gudun hijira sama da 600,000 daga makwabciyarta kasar Sudan ta kudu, kamar yadda hukumar kula da 'yan gudun hijira ta kasar Sudan (HAC) ta tabbatar da hakan.

Cikin wata sanarwa da kwamishinan HAC Ahmed Mohamed Adam ya fitar, ta ce, gwamnatin Sudan ta tanadi ton 12,000 na kayayyakin tallafi wadanda za ta rabawa 'yan gudun hijirar na Sudan ta kudu.

Jami'in na Sudan ya bukaci hukumomin kasashen waje da su marawa shirin tallafin da kasar ta Sudan ke baiwa 'yan gudun hijirar na Sudan ta Kudu, kafin zuwan damina.

A ranar 26 ga watan Maris ne, gwamnatin Sudan ta amince za ta sake bude sabon shirin ba da agaji ga mutanen dake fama da matsananciyar yunwa a Sudan ta Kudun.

Tun da farko hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD (UNHCR) da abokan huldarta suka nemi gudumowar kudi kimanin dalar Amurka miliyan 166 daga kungiyoyin ba da tallafi na kasa da kasa domin tallafawa 'yan gudun hijirar da Sudan ta karbi bakuncinsu.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China