in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Guterres ya nanata muhimmancin yin aiki tare don samar da makamashi a duniya
2017-11-02 12:23:55 cri

Sakatare janar na MDD Antonio Guterres, ya jaddada muhimmancin jajurcewa da hada karfi da karfe don yin aiki tare don samar da makamashi a duniya baki daya.

Da yake jawabi a lokacin bude babban taro a birnin New York, mista Guterres ya ce, suna son su tabbatar da cewa, an samu wani yanayi ta yadda makamashi zai kasance a matsayin babban jigon samar da dawwamamman ci gaba, kuma hakan zai tabbatar ne ta hanyar yin hadin gwiwa da yin aiki tare tsakanin kasa da kasa wajen samar da makamashi mai amfanarwa ga ci gaban muhalli wanda kuma ba zai kasance barazana game da sauyin yanayi ba.

Samar da makamashi na zamani ya kasance wani muhimmin aiki wanda zai tabbatar da rage kangin fatara, da samar da abinci, da inganta lafiyar jama'a, da kuma samar da ilmi ga kowa, ya kara da cewa, wadannan su ne ginshikai wajen samar da dawwamamman ci gaban masana'antu, da ci gaban fannin kiwon lafiya a cikin birane da kuma samun nasarar magance matsalar sauyin yanayi.

Sama da mutane biliyan guda ne suke rayuwa ba tare da hasken wutar lantarki ba a fadin duniya, kuma daga cikin adadin, akwai mutane miliyan 500 dake nahiyar Afrika, kana wasu mutanen sama da miliyan 400 dake nahiyar Asiya, sannan wasu mutanen kimanin biliyan 3 har yanzu suna yin girki da dumama gidajensu ba tare da cin moriyar kimiyyar zamani ko kuma makamashi mai tsabta ba.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China