in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Uganda na sa ido kan cutar Marburg mai kisa
2017-10-23 09:14:09 cri

Ma'aikatar lafiya ta Uganda ta ce, tana bibiyar mutane 55 da take zargin sun yi mu'amala da wadanda suka kamu da cutar Marburg.

Ministar lafiyar kasar Jane Aceng, ta shaidawa manema labarai cewa, kawo yanzu, mutane 3 ne suka kamu da cutar, inda aka tabbatar da daya daga cikinsu, daya kuma zargi ake, yayin da dayan kuma ake tsammanin ya kamu da ita, a lardin Keen dake kasar.

Ta kuma tabbatarwa al'umma cewa, kasar na da karfin yaki da barkewar cutar Marburg.

A ranar 19 ga watan nan ne aka tabbatar da barkewar cutar Marburg da ake farawa da zazzabi da zubar jinni a kasar Uganda.

An samu bullar cutar ta karshe ne a shekarar 2014 a yankunan tsakiya da yammacin kasar.

Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta bayyana cutar Marburg a matsayin matsananciya mai hadarin gaske, wanda wasu kwayoyin cuta na dangin Ebola ke haifarwa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China