Yau Litinin ne madam Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana a yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing cewa, batun samun 'yancin yankin Catalonia, harkar cikin gidan kasar Spaniya ce. Kuma kasar Sin ta fahimci kokarin da gwamnatin Spaniya take yi wajen kiyaye dinkuwar kasar, hadin kan al'umma da cikakken yankin kasar. Kasar Sin tana mara wa Spaniya baya a wannan mataki.
A kwanan baya ne, majalisar yankin Catalonia mai cin gashin kai na Spaniya ta zartas da kudurin dokar neman 'yancin kan yankin, tare da yin shelar samun 'yancin kai da neman kafa kasa. Gwamnatin Spaniya ta ce, za ta dauki matakan da suka wajaba kan lamarin, bisa tanade-tanaden da ke cikin kundin tsarin mulkin kasar. (Tasallah Yuan)