in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Alkali a Spaniya ya yanke hukuncin tura 2 daga cikin mutane 4 da ake zargi da kai hari a kasar zuwa gidan yari
2017-08-23 09:37:59 cri

Mai shari'a Fernando Andreu na Spaniya, ya yanke hukuncin da ya tura 2 daga cikin mutane hudu da suka rayu cikin 12 da ake zargi da kai hare-hare a kasar a makon da ya gabata zuwa gidan yari.

Rahoton Sky News ya ruwaito cewa, mai shari'a Andreu ya yanke hukuncin ne bayan sauraron karar.

An tuhumi wadanda ake zargin 2 da suka hada da Chemlal da Driss Oukabir da kisan kai da zama 'ya'yan kungiyar ta'addanci da kuma mallakar ababen fashewa, inda za a rike su a gidan yari ba tare da beli ba.

Mutum na 3 da ake zargi kuwa, za a rike shi na tsawon sa'o'i 72 yayin da za a ci gaba da bincike kansa.

Shi kuwa na hudun, Mohammed Aalla, an sake shi bisa rashin kwararan shaidu da za su tabbatar da laifin da ya aikata.

Mutanen hudu daga cikin 12 da ake zargi da kai hare-hare cikin makon da ya gabata a Barcelona da Cambrils, sun bayyana ne gaba babbar kotun kasar Spaniya a jiya Talata. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China