Driss Oukabir da Mohamed Aalla da Salar El Karib da Mohammed Houli Chemlal za su gurfana gaban Mai shari'a Fernando Andreu wanda shi ne ke jagorantar bincike kan al'amarin.
An kai mutanen 4 garin Tres Cantos, wanda ke wajen birnin Madrid jiya da daddare, inda a yau za a tura su gidan yari domin jiran shari'ar da za a yi musu game da rawar da suka taka wajen kai harin.
Mutanen 4 su ne wadanda suka rayu daga cikin mutane 12 da ke da hannu wajen kai hare-haren, wanda ya kuma raunata fiye da mutane 120 a yankin Catalan na Spaniya. (Fa'iza Mustapha)