Firaiministan yace babu wani batu na kuri'ar raba gardama, kuma ya nanata cewa, kasarsa tana da cikakken karfinta, kuma za'a yi amfani da dukkan albarkatun kasar don kaucewa duk wani nau'i na neman tsokana ko tada zaune tsaye a kasar.
Yace batun kada kuri'ar raba gardaman ta haifar da wata irin halayya ta yadda babu wani dan kasar da zai yarda da ita, muddin yayi amanna da tsarin mulkin demokaradiyya, kuma ana zargin shugabannin yankin na Catalan da haddasa rikicin.(Ahmad Fagam)