in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi kira a samar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu
2017-10-25 10:06:30 cri

Manzon musamman na babban sakataren MDD a kasar Sudan ta Kudu David Shearer ya yi kira ga jagororin kasar, da su jingine duk wani bambance-bambancen siyasa dake tsakaninsu, don ganin sun dawo da zaman lafiya a fadin kasar, yayin da ma'aikata a kasar suka bi sahun ragowar kasashen duniya wajen murnar ranar MDD a birnin Juba.

Ya kuma yi kira ga gwamnatin rikon kwaryar kasar da bangarorin da ba sa ga maciji da juna, da su kasance masu kishin kasa, kana su kare martaba da rayukan al'ummominsu.

Ya ce, taron sasantawan da aka kira zai taimakawa shirin samar da zaman lafiyar kasar.

A jiya ne ma'aikatan MDD dake aiki a sassan kasar Sudan ta kudu suka hadu da al'ummomi da shugabannin yankunan kasar, don bikin ranar MDD da kuma irin ayyukan da MDDr take yi na kare rayukan fararen hula, da samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma ci gaba tsakanin matasan kasar.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China