in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
"Dangantakar dake tsakanin Sin da Najeriya tana samar da damammaki ga al'ummomin kasashen biyu"inji Dr. Orji Uzor Kalu
2017-10-27 18:18:26 cri

Wani hamshakin dan kasuwar Najeriya mai rukunin kamfanonin SLOK, Dr. Orji Uzor Kalu, ya bayyana muhimmanci karfafa dangantakar cinikayya tsakanin Sin da Najeriya bisa la'akari da dadadden tarihin dangantakar cinikayya dake tsakanin kasashen biyu.

Dr. Uzor Kalu ya bayyana hakan ne a lokacin gabatar da lacca mai taken "fadada hanyoyin tattalin arziki, da rawar da kamfanoni masu zaman kansu da gwamnati zasu taka, wanda a gabatar a yau Juma'a a jami'ar nazarin harkokin kasuwanci da tattalin arziki ta kasa da kasa ta Beijing UIBE dake kasar Sin.

A zantawar da yayi da wakilin sashen Hausa na CRI, Ahmad Fagam, DR. Uzor Kalu ya bayyana cewa akwai kamfanonin kasar Sin masu yawa dake gudanar da ayyuka a Najeriya, musamman kamfanonin gine-gine dana sadarwa da dai sauransu. A cewarsa nadin sabon jakadan da Najeriyar tayi zuwa kasar Sin zai taimaka matuka wajen karfafa dangantarkar cinikayya tsakanin kasashen Sin da Najeriya.

Bugu da kari, ya nanata alfanun karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu musamman a fannonin kimiyya da fasaha, aikin gona, da sauran fannoni.

Dr. Uzor Kalu yace kamata yayi Najeriya ta koyi fasaha daga kasar Sin musamman a fannin aikin gona da sarrafa amfanin gona.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China