in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Putin ya taya Xi Jinping murnar sake zama babban sakataren JKS
2017-10-26 13:36:53 cri

Jiya Laraba 25 ga wata agogon kasar Rasha, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya aika wa Xi Jinping sakon taya shi murnar sake zama babban sakataren JKS.

A cikin sakon nasa, mista Putin ya ce, sakamakon zaben ya tabbatar da martabar mista Xi Jinping ta fuskar siyasa, ya kuma nuna cewa, manufar da Xi Jinping ya gabatar dangane yadda za a gaggauta raya tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasar Sin da daga matsayin kasar a duniya ta samu amincewa sosai.

Mista Putin ya kara da cewa, ya yi imani cewa, kudurin da aka tsai da a yayin babban taron wakilan JKS karo na 19 zai taimaka wajen inganta huldar abokantaka da hadin gwiwa a tsakanin Sin da Rasha bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni. Ya kuma yi fatan cewa, za a ci gaba da kyautata hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen 2 a sassa daban daban, a kokarin da kasashen 2 ke yi na taimakawa juna wajen daidaita al'amuran shiyya-shiyya da kasa da kasa. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China