in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bukaci sassan da ke gaba da juna a Libya da su sasanta
2015-11-03 10:10:33 cri

Tawagar MDD da ke kasar Libya UNSMIL a takaice ta yi kira ga sassan da ke gaba da juna a kasar Libya da su yi kokarin cimma yarjejeniyar da za ta kai ga kafa gwamnatin hadin kan kasa.

Tawagar wadda ta yi wannan kira cikin wata sanarwa, ta kuma yi kira ga manyan masu fada a ji a kasar ta Libya da su yi kokarin shirya zaman sasantawa domin samun nasarar cimma yarjejeniyar kafa gwamnatin hada kan kasa ta yadda za a farfado da shirin mika mulki ga zababbiyar gwamnati.

Majalisun dokokin kasar biyu da ke gaba da juna dai sun shafe sama da shekara guda suna tattaunawa kan yadda za a shimfida zaman lafiya a kasar, ba tare da wani kyakkyawan sakamako ba.

MDD ma ta sha yunkurin ganin an kafa gwamnatin hada kan kasa ko dai bangarorin biyu su amince da wannan mataki ko kuma su yi fatali da shi baki daya.

Ko da yake manzon musamman na MDD mai kula da batun Libya Bernandino Leon ya ce, akwai alamar haske, amma dai akwai sauran rina a kaba.

Dukkan 'yan majalisun dokokin kasar biyu da ke gaba da juna sun yi fatali da shawarar da MDD ta gabatar ta kafa gwamnatin hadakar. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China