in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabon wakilin MDD ya gana da shugabannin gwamnatoci biyu a Libya
2015-11-23 09:46:37 cri

Sabon wakilin MDD na musamman a kasar Libya Martin Kobler, ya gana da shugabannin gwamnatocin kasar biyu a ranar Asabar din nan, inda ya bukace su da su amince a ci gaba da taron tattaunawar sulhu wanda ya gamu da cikas na tsawon wata guda.

Kobler, ya tattauna kan sabon ci gaban da aka samu yayin tattaunawa da bangaren gwamnati da majalisar dokokin kasar wacce ke samun goyon bayan kasashen duniya dake birnin Tobruk a gabashin kasar. Sannan a wannan rana ne ya zarce zuwa birnin Tripoli domin ganawa da bangaren gwamnatin 'yan aware masu kaifin kashin Islama na kasar.

Kasar mai dunbun albarkatun man fetur, tana fuskantar zaman tankiya ne yayin da kan gwamnati da na majalisar kasar ya rabu biyu, wato bangaren masu kaifin kishin Islama wanda da ke birnin Tripoli da 'yan tawaye ke jagoranta da kuma bangaren dake samun goyon bayan MDD dake Tobruk.

A ganawarsa karon farko a Libyan, Kobler ya jaddada cewar, zai dora ne daga inda wanda ya gada Bernardino Leon ya tsaya.(Ahmed Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China